Ka da a zargi van Gaal - Jesse Lingard

Image caption Louis van Gaal

Dan wasan Manchester United, Jesse Lingard ya ce bai kamata a dora wa kociyan kungiyar, Louis van Gaal laifi ba saboda matsalolin da Man United din take fuskanta.

Lingard ya ce " ba laifin kociya ba ne, tun da dai mun je filin buga wasa."

Jesse Lingard ne dai ya zura wa Stoke City kwallon farko a minti 14 da fara wasan da suka ci Stoke 3 - 0, a ranar Talata.

Yanzu haka, Manchester United din ita ce ta biyar amma kuma akwai tazarar maki biyar tsakaninta da kungiyoyi hudu da ke samanta a teburin Premier.

Kafin wannan lokacin dai manchester ta buga wasanni 11 amma ba tatre da ci ba a farkon fara wasa.