Falcao ba zai yi wa Chelsea wasa ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau daya kawai Falcao ya buga wasa a gasar Premier tunda Chelsea ta sayo shi daga Monaco a watan Yulin da ya gabata.

Ba a sanya sunan Radamel Falcao a cikin jerin 'yan wasan Chelsea 25 da za su buga wasa a matakin sili-daya-kwale na gasar Zakarun Turai ba.

Dan wasan, dan kasar Colombia, bai buga wasa ba tun daga watan Oktoba saboda raunin da ya yi a cinyarsa , kuma an maye gurbinsa da sabon dan wasan da kungiyar ta karbo aro, Alexandre Pato.

Sau daya kawai Falcao, mai shekara 29, ya buga wasa a gasar Premier tun lokacin da kungiyar ta sayo shi daga Monaco a watan Yulin da ya gabata.

A makon jiya ne kungiyar ta Chelsea ta karbi aron tsohon dan wasan AC Milan Pato, mai shekara 26, na tsawon wata shida daga kungiyar Corinthians.

Sai dai dan wasan dan kasar Brazil bai buga wasa ko daya ba tun daga watan Nuwamba saboda ana jira ya murmure bayan jinyar da ya yi.

Kociyan rikon-kwarya na Chelsea Guus Hiddink ya sanya sabon dan wasa Matt Miazga a cikin 'yan wasan da za su murza leda a gasar Zakarun Turai da ta Premier.