Muna neman tsira ne - Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsene Wenger

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya yarda cewa kulob din nasa na neman tsira ne a gasar Premier, bayan da Arsenal din ta tashi canjaras da Southampton wato ba bu ci a wasan ranar Talata.

Arsene ya ce "dole ne mu tashi tsaye kuma muna da kalubale a gabanmu musamman idan za mu yi wasa a waje ne ba gida ba."

Arsenal dai ba ta yi zarra a wasanni hudu na Premier ba sannan kuma ba ta ci ko da kwallo daya ba wasanni uku da ta buga.

kungiyar ce da ta hudu a teburin Premier kuma akwai tazarar maki 5 tsakaninta da mai matsayi na daya wato Leicester.