Aston Villa ta yi sabon kamu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aston Villa

Tsohon gwamnan bankin Ingila, Lord King ya shiga kwamitin darektocin kungiyar wasa ta Aston Villa.

Mr. King, mai shekara 67 dai ya dade yana goyon bayan Aston Villa wadda take kasan teburin gasar Premier ta Ingila.

Shugaban kungiyar ta Aston Villa, Steve Hills ya ce " Lord King ya jagoranci bankin na Ingila har aka kai ga gaci duk da cewa an fuskanci matsananciyar matsalar tattalin arziki a duniya."

Ya kara da cewa " saboda haka sanya shi a kwamitin darektocin zai taimaka mana wajen kai wa ga gaci."

Shi ma Lord ya ce " zan yi iya bakin kokarina wajen dawo da kimar Aston Villa."