Serie A: An tsai da wasa saboda wariyar jinsi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasan Napoli da Lazio

Mai busa wasa, a wasan da Napoli da Lazio suka tashi 2-0, ranar Laraba a gasar Seria A ta Italiya, ya tsayar da wasan har na minti uku saboda ihu da wasu magoya bayan Lazio suka yi wa dan wasan Napoli, Kalidou Koulabaly, a lokacin da ya taba kwallo.

Rafalin, Massimiliano Irrati ya yarda a cigaba da buga wasa bayan da ya tuntubi kociyoyi da shugabannin kungiyoyin.

Koulabaly ya ce " Ina son mika godiyata ga 'yan wasan Lazio, amma godiya ta musamman ga Irrati bisa jajircewarsa."

Khalidou Koulabaly dai wanda dan kasar Senegal ne ya fara wasan kwallo a Metz sannan kuma ya koma Napoli daga kulob din da ke Belgium Genk a 2014.