CAF ta ɗaga hannun Salman a zaben FIFA

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sheikh Salman na bukatar goyon bayan nahiyar Asiya domin samun nasara

Hukumar da ke kula da kwallon Afrika, CAF ta ce za ta goyi bayan dan Bahrain, Sheikh Salman Bin Ebrahim Al-Khalifa a takararsa ta shugabancin FIFA.

Kasashe hamsin da hudu ne ke cikin CAF, kuma nahiyar ce ta fi kowacce yawan kuri'u.

Hudu daga cikin mutane biyar da ke sa ran maye gurbin Sepp Blatter, duk sun halarci taron CAF a Rwanda domin kamun kafa.

Sheikh Salman na daga cikin manyan 'yan takara tare da babban abokin hammayarsa Gianni Infantino na kasar Switzerland, wanda nahiyar Turai ke goyon bayansa.

A lokacin taron koli na FIFA ne, za a zabi sabon shugaba a birnin Zurich a ranar 26 ga watan Fabarairu.

Matakin na CAF na nuna cewa nahiyar Afrika ta yi buris da wani dan nahiyar da ke takara watau Tokyo Sexwale na Afrika ta Kudu.