Batun City ba zai dauke hankali na ba — Guardiola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Guardiola tare da Pellegrini

Kocin Bayern Munich Pep Guardiola ya ce batun zai koma Manchester City ba zai dauke hankalinsa a kakar wasa ta bana ba.

Guardiola mai shekaru 45, ya kulla yarjejeniyar shekaru uku tare da City domin maye gurbin Manuel Pellegrini a kakar wasa mai zuwa.

Tsohon kocin Barcelona din ya lashe kofuna 19 a cikin shekaru shida.

"Babu matsala, zan yi magance duka batutuwan biyu," in ji Guardiola.

A bara ne Guardiola ya bayyana cewa zai bar Bayern domin komawa Ingila.