Magoya bayan Liverpool za su yi bore

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Magoya bayan Liverpool na ganin da bata kara kudin tikitin ba da ta bayar da kyakkyawan misali

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool sun shirya barin filin wasa na Anfield, domin nuna adawa a lokacin taka leda tsakanin Liverpool da Sunderland a gasar Premier League.

Kungiyar masu kallon kwallo ta Spion Kop 1906 - wadda ke samun goyon bayan ta Spirit of Shanky(SoS) - ta bai wa magoya bayan Liverpool shawarar cewa su fice daga filin wasa a daidai minti 77 da fara wasan, domin nuna adawa da sayar da tikitin kallon wasa a babban wajen 'yan kallo a kan kudi Fam 77.

Liverpool din dai ta sanar da karin kudin tikitin ne wanda zai fara aiki a kakar wasannin da ke tafe zuwa Fam 59.

Wata sanarwa da ta fito daga kungiyar SoS ta bayyana fushinta na rashin "wani bayani" daga masu kungiyar wasan.

Sanarwar ta kara da cewa "Mun yi imanin cewa rage kudin tikiti adalci ne ta yadda zai sa masoya kwallo su ci gaba da ba da goyon baya a filin wasa na Anfield."