'Sturridge bai shirya murza leda ba'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sturridge ya haskaka a shekarar 2015

Dan kwallon Liverpool Daniel Sturridge bai shirya buga wasa ba, duk da cewar ya koma atisaye, in ji kocinsa Jurgen Klopp.

Sturridge mai shekaru 26, bai murza leda ba tun a farkon Disambar bara.

"Daniel ya koma horo kuma abubuwa na tafiya daidai," in ji Klopp.

Sturridge ya buga wasanni shida a kakar wasanni ta bana, amma rauni ya hana shi ci gaba da wasa.

Suma 'yan wasan Liverpool Divock Origi da kuma Philippe Coutinho duk sun koma horo.