Donetsk za ta sayar da Teixeira kan £38.4m

Hakkin mallakar hoto UNIAN
Image caption Alex Teixeira ya zama tauraron kwallon kafa na baya bayan nan da ya koma China.

Kungiyar kwallon kafa ta Shakhtar Donetsk ta amince ta sayar da dan wasanta Alex Teixeira ga kulob din Jiangsu Suning na kasar China a kan kudi Fam 38.4 miliyan.

Dan wasan tsakiyan kuma dan asalin kasar Brazil, har ila yau wanda kungiyar Liverpool ta so saya, ya zamo tauraron kwallon kafa na baya-bayan nan da ya koma wasa a China.

A kwanan nan ne tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea Ramires da tsohon dan wasan gaba na Atletico Madrid Jackson Martinez suka koma China.

Kudin da aka sayi Teixeira mai shekara 26 ya zarta wanda aka sayi Martinez wato Fam 31 miliyan a farkon makonnan.

Kuma wannan ne karo na uku da wata kungiyar da ke buga wasa ta rukunin Super League ta sayi dan wasan da ya fi kowanne tsada a cikiin kwanaki 10, kafin a rufe kasuwar sayar da 'yan wasa a ranar 26 Fabrairu.

Jiangsu Suning ta sayi Ramires a kan Fam 25 miliyan, yayin da Guangzhou Evergrande Taobao ta sayi Martinez.

Liverpool ta so sayen Teixeira a lokacin da aka bude kasuwar sayar da 'yan wasa a watan Janairu, yayin da Shakhtar ta yi ikirarin cewa Liverpool ta yi watsi da tayin sayen shi a kan kudi Fam 24 miliyan.