Liverpool: Klopp ba zai ga wasa ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp ba zai halarci filin wasa na Anfield ba domin kallon buga wasan da kungiyar ta Liverpool za ta da Sunderland a ranar Asabar, sakamakon matsalar cutar tsakuwa da ke shafar hanji wato Appendicitis.

Yanzu haka dai sauran manyan jami'an kulob din ne za su sanya ido don ganin wasan ya tafi dai-dai.

Jami'an dai su ne Zeljko Buvac da Peter Krawietz da Pepijn Lijnders da kuma John Achterberg.

Shi dai Jurgen Klopp, mai shekara 48 ya ci wa Liverpool wasanni shida na Premier tun bayan da ya maye gurbin Brendan Rogers, a watan Octoba.