Leicester ta lallasa Man City

Image caption Roberto Huth ne ya ci kwallaye 2

Leicester wadda ita ce kungiya ta daya a saman teburin gasar Premier ta lallasa mai biye mata a teburin Manchester City da ci 3 -1.

Dan wasan Leicester Roberto Huth ne dai ya ci kwallon farko da ta biyu sannan Mahrez kuma ya zura ta uku, a ragar ta Man City.

Sai dai kuma dan wasan Manchester, Sergio Aguero ya samu ya ci wa kungiyar tasa kwallo daya kafin a karkare wasan.