CHAN 2016: Congo ta dauki kofi

Image caption DR. Congo ta dauki kofin CHAN

Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta dauki kofin gasar nahiyar Afirka ta 'yan gida wato CHAN, bayan da ta lallasa Mali da ci 3-0, a wasan karshe, da yammacin Lahadi, a Kigali, babban birnin Rwanda.

Dan wasan Congo, Meshack ne dai ya fara jefa kwallon farko a ragar ta Mali, minti 29 da fara wasa. Meshack din ne dai ya kuma kara ta biyu. Jonathan Bolingi ne ya zura ta uku.

Wannan dai shi ne karo na biyu da DR Congon take lashe kofin gasar wadda aka fara a 2009.

A 2009 ta dauki kofin bayan da ta doke Ghana da ci 2-0.