CHAN 2016: Ivory Coast ta doke Guinea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Ivory Coast

Ivory Coast ta cancanci samun matsayi na uku, a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan gida wato CHAN, bayan da ta doke Guinea da ci 2-1.

Mai tsaron ragar Ivory Coast, Abdoul Keita ne dai ya fara cin kasar tasa bayan da ya yi kuskuren bin kwallon, kafin daga bisani dan wasan Ivory Coast, Badie Gbagnon ya jefa ta biyu.

Alseny Bangoura na Guinea ne ya samu zarafin jefa kwallo daya a ragar Ivory Coast.

Mai tsaran ragar Ivory Coast, Abdoulaye Cisse ne dai ya zamo gwarzo a wasan bayan da ya kade kwallaye har biyu a dukan fanareti.