Ban yarda Mourinho zai gaje ni ba - van Gaal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho da van Gaal

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal ya ce bai yarda da rahoton da ke cewa sunan tsohon kociyan Chelsea, Jose Mourinho na cikin jerin sunayen da za su karbi kujerarsa.

Van Gaal ya ce " ban yarda akwai wata alaka tsakanin Mourinho da United ba."

Shi dai Mourinho wanda aka kora daga Chelsea a watan Disamba ya ce zai dawo don cigaba da horas da 'yan wasa, bayan da aka bayyana cewa wakilansa sun tattauna da shugabannin Manchester United.

A yammacin ranar Lahadin nan dai Chelsea za ta karbi bakuncin Man Utd.