Premier: Bai kamata a kara kudin tikiti ba - Shearer

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Tsohon dan wasan Ingila, Alan Shearer

Tsohon dan wasan Ingila, Alan Shearer ya ce bai kamata a kara kudin tikitin shiga kallon wasanni gasar Premier ba a kakar wasanni ta gaba.

Shearer ya ce " ba na tunanin za a tambayi duk wani mai goyon bayan wata kungiya da ya biya karin kudin tikiti a kakar wasan mai zuwa."

Ya kara da cewa " kamata ya yi su rinka samun tikitin a kan kudi £10 ko kuma £20."

Dubban magoya bayan Liverpool sun fita daga wasan da kungiyar ta buga da Sunderland a Anfield ranar Asabar sakamakon tsadar tikitin wanda aka sayar a kan £77.

Hakan dai ya faru ne bayan da hukumomin da ke kula da gasar Premier League suka sayar wa masu talbijin 'yancin watsa wasannin, a 2015, a kan £5.14bn wanda kuma zai fara aiki daga kakar wasanni ta 2016-2017.