Enrique na gab da kafa sabon tarihi a Barca

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Enrique tsohon dan wasan Barcelona da Real Madrid ne

Kocin Barcelona Luis Enrique ya ce "har yanzu akwai sauran aiki" a kakar wasa ta bana, bayan da ya buga wasanni 28 ba tare da an samu galaban a kansa ba.

Enrique ya jagoranci Barcelona ta lashe wasanni 10 a jere, kuma idan har ya doke Valencia a ranar Laraba, to zai kafa sabon tarihi fiye da tsohon kocin kungiyar Pep Guardiola a shekara ta 2010 zuwa 2011.

"Ban damu da alkaluma ba, ina son mu cimma burinmu a karshen kakar wasa ta bana," in ji Enrique.

Barcelona ta lashe kofuna uku a kakar wasa ta farko da Enrique ya jagoranta, kuma a yanzu haka su ne kan gaba a teburin gasar La Liga.