Za a warware batun tsadar tikiti - Klopp

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce za a samo bakin zare dangane da matsalar da aka samu ta tsadar tikitin shiga kallon wasa, a Anfield.

A ranar Asabar ne dai dubban magoya bayan Liverpool suka fice daga filin da kungiyar ta yi canjaras da Sunderland wato 2-2.

Wata kungiyar magoya baya ce ta umarci masu kallo da su fice daga filin wasan a minti 77 na wasan, domin nuna rashin amince wa da £77 na tikitin shiga kallon wasa da zai fara a kakar wasanni mai zuwa.

Klopp ya ce " dole ne mu warware matsalar. Ba ma son mutane su rinka barin filin wasa gabanin kammala wasan."