Shin ko Leicester za ta dauki kofin Premier?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Leicester, Jamie Vardy

Leicester wadda yanzu haka ita ce a saman teburin Premier kuma ta ba wa mai biye mata wato Tottenham tazarar maki biyar, ta zamo kungiyar wasa da jama'a suke ta nuna al'ajabi kan makomarta, a karshen gasar ta Premier.

Tun dai bayan da ta casa Manchester City a gida da ci 3-1 ranar Asabar, likkafarta ta kara gaba.

Yanzu haka dai wasanni 13 suka rage wa kulob din ya buga wadanda idan ya ci su to zai dauki kofi.

A ranar Lahadi mai zuwa ne Leicester din za ta je gidan Arsenal domin karawa da ita.

Kuma idan har ta samu nasara a kan Arsenal din to ana ganin babu makawa za ta iya kaiwa ga daukar kofi.

Leicester dai ba ta taba daukar kofin Premier ba kuma kafin wannan lokacin ta kasance kurar baya a gasar ta Premier ta Ingila.