Matar Andy Murray ta haihu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Andy Murray ya ce matarsa da 'yarsa sun fi komai muhimmanci a gare shi.

BBC ta fahimci cewa Kim Sears, matar fitaccen dan kwallon Tennis, Andy Murray, ta haifi 'ya mace.

An fahimci cewa Sears ta haifi 'yarsu ta fari ne ranar Lahadi da daddare.

A watan Afrilun da ya wuce ne aka daura aurensu a garin Dunblane, mahaifar Murray, kuma sun bayyana cewa matar tana da juna-biyu ne a lokacin bazara.

Gabanin fara gasar Australian Open ta watan jiya ne Murray, wanda a yanzu shi ne dan kwallon Tennis na biyu a duniya, ya ce zai bai wa iyalinsa "muhimmanci."

Ya ce: "Da na ya fi muhimmanci a gare ni, mata ta ma ta fi muhimmanci a wuri na a kan kwallon tennis."