Liverpool ba ta damu da magoya baya ba - Evans

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Magoya bayan Liverpool

Tsohon kociyan Liverpool, Roy Evans ya yi kira da kungiyar da ta ba wa magoya baya mahimmanci.

A ranar Asabar ne dai dubban magoya bayan Liverpool din suka fice daga filin wasa, a lokacin da take karawa da Sunderland, a Anfield saboda batun karin kudin tikitin shiga kallon wasa.

Roy Evans ya ce " ya kamata a cire batun kudi a koma maganar taka leda."

Evans wanda ya jagoranci kungiyar a 1990 ya kara da cewa " ba zai yiwu ba a cigaba da raina magoya baya ba."