Messi na fama da matsalar ƙoda

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Messi ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya a 2015

Dan kwallon Barcelona Lionel Messi bai shiga atisaye ba a ranar Litinin saboda ya na fama da matsala a kodarsa.

An yi masa gwaje-gwaje a kodarsa, kuma sai a ranar Laraba zai koma horo.

Dan wasan na Argentina ya fuskanci matsalar koda a cikin watan Disamba abin da aka danganta da 'tsakuwar koda'.

Wata sanarwa daga Barcelona ta ce Messi mai shekaru 28, zai koma 'wasa' a ranar Laraba.

"Za a yi wa Lionel Messi gwaje-gwaje a ranar Litinin da Talata domin sake duba kodarsa," in ji sanarwar.

Messi ya zura kwallaye 12 a wasanni 17 na gasar La Liga.