Chelsea: Zuwa wasan karshe ne mafita - Courtois

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mai tsaron ragar Chelsea, Thibaut Courtois

Mai tsaron ragar Chelsea, Thibaut Courtois ya ce dole ne kulob din ya kai ga wasan karshe na Champions League ko kuma gasar cin kofin hukumar wasan kwallon kafa ta Ingila wato FA Cup, idan dai har tana son kwatar kanta a wannan kakar wasan.

Ranar 16 ga watan Fabrairu ne dai Chelsea za ta kara da paris St-Germain, kafin ta buga wasan zagaye na biyar na gasar FA Cup da Manchester City.

Courtois ya ce " za mu yi gamo da manyan kungiyoyi guda biyu saboda haka dole ne mu kokarta mu ci wasannin."

Ya kara da cewa " hanya daya da za mu iya tsira a wannan kakar ita ce mu dangana ga wasan karshe na Champions League ko kuma FA Cup."

Chelsea dai ita ce mai matsayi na 13 a teburin Premier sannan tana da maki 17 ne kacal a gasar Champions League.