Ba zan bar Real Madrid ba - Ronaldo

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ronaldo ya bayyana farin cikinsa kan karbar lambar yabon Pichichi

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya ce ba zai bar kungiyar ba kafin kwantiraginsa ya kare a shekarar 2018.

An sha danganta Ronaldo mai shekaru 31 kuma dan kasar Potugal da tsohuwar kungiyarsa wato Manchester United, wadda ta sayar da shi ga Real a shekarar 2008 da kuma St-German.

"Ina so in ci gaba da kasancewa a Real nan da shekaru biyu masu zuwa. Ina maganar zuwa karshen kwantiragina, abin da zai biyo baya, sai mu jira mu gani." In ji kyaftin din.

Ronaldo ya bayyana hakan ne a lokacin wani biki na karba lambar yabo na Pichichi, wanda ya lashe kasancewarsa wanda ya jefa kwallo mafi yawa 48 a gasar La Ligar da ta wuce.

Dan wasan ya kara da cewa "Wannan ce gasar League mafi girma a duniya, ko da yake na yi wasa a gasar premier League."