Newcastle: Jonjo Shelvey ya ci kudinsa - Rahoto

Image caption Dan wasan Newcastle, Jonjo Shelvey

Wani bincike da cibiyar nazari kan harkokin wasanni ta duniya da ke zaune a Switzerland wato CIES ta gudanar, ya nuna cewa kungiyar Newcastle ce ta sayi dan wasan da ya fi dacewa da kudin da aka saye shi, a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu.

Newcastle din dai ta sayi dan wasan tsakiya na Swansea, Jonjo Shelvey a kan £12m, wanda kuma a cewar cibiyar farashin dan wasan mai shekara 23 ya kai £23.5.

Sai dai kuma binciken ya ce Newcastle din ya cika ruwa da ya fanshi dan wasan Ingila, Andros Townsend a kan £12m.

Nazarin ya kara da cewa kulob din Guagzhou Evergrande ya wuce gona da iri da ya kashe £31m a kan dan wasan Atletico Madrid, Jackson Martinez.

Ita ma Bournmouth, kamar yadda nazarin ya ce ta zuba kudi fiye da kima a kan dan wasan Norwich, Lewis Grabban.