Dole mu doke Espanyol - Neville

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan Valencia, Gary Neville

Kociyan Valencia, Gary Neville ya ce dole ne kungiyarsa ta doke Espanyol a ledar da za su taka ranar Asabar, domin gujewa kara fadowa kasa daga teburin La Liga.

Yanzu haka Valencia ita ce ta 14 teburin gasar Champions League kuma tana gab da kara silmiyowa.

Kuma kungiyar ba ta ci wasanni hudu ba sannan ta yi canjaras a guda biyar duk a karkashin jagorancin Neville wanda aka nada a farkon watan Disamba.

Neville ya ce " dole ne mu ci wasanmu na ranar Asabar."