Zika: Kenya ka iya janyewa daga Olympics

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A makon jiya ne hukumar lafiya ta duniya ta ayyana dokar ta-baci a kan cutar

Akwai yiwuwar kasar Kenya ta janye daga wasannin bazara na Olympics da za a yi a birnin Rio na kasar Brazil, muddin cutar Zika ta zama annoba, a cewar shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar.

Ana danganta haihuwar yara masu nakasa a Kudancin Amurka da cutar ta Zika da sauro ke yadawa.

Kipchoge Keino ya bayyana cewa, "Ba za mu yi kasadar kai 'yan wasan Kenya can ba, muddin cutar ta kai matsayin annoba."

Hukumomin Brazil din dai sun jaddada cewa 'yan wasan guje-guje da 'yan kallo ba za su fuskanci hadarin kamuwa da cutar ba, sai dai mata masu juna-biyu.

Kwamitin kasa da kasa mai shirya wasannin na Olympics ya ce yana sa ido sosai a kan masu shirya gasar, kuma za a duba wuraren yin wasan kullum kafin fara gasar da kuma lokacin yinta.