Kurt Zouma zai yi jinyar wata shida

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan kasar ta Faransa ya buga wa Chelsea wasanni 32 a kakar wasannin nan

Dan wasan baya na kungiyar Chelsea, Kurt Zouma, zai shafe wata shida ba tare da murza leda ba saboda raunin da ya samu a kwauri wanda ke bukatar a yi masa tiyata.

Zouma ya fadi ne bayan ya yi yunkurin dukan kwallo da ka, a wasan da suka yi da Manchester United a ranar Lahadin da ta wuce, wanda suka tashi ci 1-1.

An kuma dauke shi a kan gadon daukar marasa lafiya, sannan aka fitar da shi daga filin.

Zouma ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa "Hoton raunin da aka dauka a yau ya nuna cewa na ji rauni a bargo na. Za a yi mini tiyata a wannan makon kuma zan dawo da karfi na."

Kungiyar ta Chelsea dai ta ce zai kwashe wata shida bai yi wasa ba.

Daya daga cikin wasannin baya-bayan nan da ya buga wa Faransa sun hada da wasan sada zumunci da Denmark, a watan Oktoba.