Sunderland: Johnson ya amsa laifin lalata yarinya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Sunderland, Adam Johnson

Dan wasan Sunderland, Adam Johnson ya amsa laifi daya daga cikin laifuka uku da ake tuhumarsa da su masu dangantaka da lalata da yarinya 'yar kasa da shekara 16.

Sai dai kuma, Adam mai shekara 28, wanda ya bayyana a gaban wata kotun Bradford ya ki amincewa da sauran laifuka guda biyu.

A watan Maris na 2015 ne dai aka kama Mista Johnson a garinsa na Durham da ke Castle Eden.

Mista Johnson wanda aka haifa a Sunderland ya fara harkar kwallon kafa a Middlesbrough kafin ya koma Manchester City, sannan kuma a shekarar 2012 ya je Sunderland, a kan £10m.