Liverpool: An soke karin kudin tikiti

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Yanzu kuin shiga kallo ya zama £59

Masu kungiyar wasa ta Liverpool sun soke karin kudin tikitin shiga kallon wasa na £77 sannan kuma sun nemi afuwa dangane da rashin jin dadin da sanarwar yin karin ta haifar, ranar Asabar.

Dubban magoya bayan Liverpool ne dai suka fice daga filin wasa, lokacin da kulob din yake tsakiyar karawa da Sunderland saboda an ce za a kara kudin tikiti.

Yanzu haka farashin tikitin zai kama £59.

Kuma kulob din ya soke banbancin kudin magoya baya da na 'yan adawa, a inda kowa zai biya farashi bai daya.