Za a ci tarar Sunday Oliseh

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oliseh zai tuntubi lauyoyinsa domin kalubalantar tarar.

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria za ta ci tarar kociyan kungiyar Super Eagles ta Najeriya, Sunday Oliseh, dala dubu 30, kwatankwacin Naira miliyan 9, saboda maganganun da ya yi a wani bidiyo da aka saki ta kafar YouTube, a karshen mako.

Sai dai Oliseh zai tuntubi lauyoyinsa domin kalubalantar tarar.

Shi dai Oliseh, mai shekarar 41 ya sanya wani bidiyo ne a kan shafinsa na intanet domin mayar da martani dangane da abin da ya kira hauka irin na masu sukar sa.

Tun bayan da Guinea ta doke Najeriya da ci 2-1 a wasan zagaye na cin kofin nahiyar Afrika ta 'yan gida wato CHAN, Oliseh yake ta samun matsin lamba.

Oliseh dai ya nemi gafarar hukumar ta NFF kan babatun da ya yi da manufar mayar wa kafafen watsa labaran kasar da wasu tsoffin abokan wasansa martani.

A shafinsa na twitter, Oliseh ya ce maganar da nayi a kan masu sukar ra'ayina, ba ina nufin gaba daya 'yan Najeriya ba ne. Ba zan taba danganta 'yan kasata da hauka ba."

A watan Yuli ne dai tsohon kyaftin din Najeriyar, Oliseh ya karbi jagorancin Super Eagles daga hannun Stephen Keshi.