West Ham ta kafa tarihi — Bilic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Slaven Bilic ya ce gwara su dauki Kofin FA a kan su shiga sawun manyan kungiyoyin Premier.

Kociyan West Ham Slaven Bilic ya ce dokewar ba-zatar da kungiyarsa ta yi wa Liverpool a gasar cin Kofin FA na daya daga cikin abubuwan da ba za su taba mantawa da shi ba a tarihin wasansu.

West Ham ta yi nasara a kan Liverpool ne da ci 2-1.

Bilic ya ce, "Wannan wasa zai zama daya daga cikin wadanda West Ham ta kafa tarihi a kansu. Hakan kuwa ya faru ne saboda mun zura kwallo a minti na karshe."

West Ham bata taba doke Liverpool a gasar cin Kofin FA, kuma bata dauki kofin ba cikin shekara 36 da suka wuce.

A ranar Lahadi ne za su fafata da Blackburn a zagaye na biyar na gasar.

A farkon shekarar nan ne Bilic, mai shekara 47, ya ce ya fi son su dauki Kofin FA a kan su zama daya daga cikin kungiyoyi hudu da ke saman teburin gasar Premier ta Ingila, wadanda ke zuwa gasar cin Kofin Zakarun Turai.