Zaben Fifa: Bility ya goyi bayan Ali

Hakkin mallakar hoto
Image caption Bility dai bai samun nasara a karar da ya shigar kan hana shi tsayawa takara ba.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Laberiya Musa Bility ya nuna goyon bayansa ga Yarima Ali na Jordan a zaben shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya da za a yi a wannan watan.

Bility ya nuna goyon bayan nasa a aikace ta hanyar halartar wani taron manema labarai da Yarima Ali ya kira a birnin Geneva ranar Alhamis.

An dai hana Bility tsayawa takarar shugabancin hukumar bayan ya kasa cika sharuddan ''dattako'' da ake son dan takarar shugabancin hukumar ya cika.

Mr. Bility dai ya ce sanarwar da Hukumar Kwallon Kafa ta nahiyar Afrika CAF ta fitar cewa tana marawa takarar Sheikh Salman baya, ''katsalandan ne da kokarin razana'' wasu.

Karin bayani