Bordeaux ta dakatar da 'yan wasanta 2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nantes ta doke Bordeaux din ne a gasar Coupe de France

Kungiyar kwallon kafa ta Bordeaux da ke kasar Faransa ta dakatar da mai tsaron gidanta Lamine Sane da kuma golanta Jerome Prior har sai abin da hali ya yi.

Kungiyar ta ce ta dakatar da 'yan wasan biyu ne sakamakon wani abu da ya faru a dakin canza tufa bayan Nantes ta doke ta da ci 4-3 ranar Laraba.

Sai dai kungiyar ta ce ba za ta yi wani karin bayani ba game da lamarin.

Ana jin wannan dakatarwar za ta iya kawo karshen zaman Sane dan kasar Senegal a kungiyar ta kasar Faransa.

Ya dai fara buga mata wasa ne a shekarar 2009 amma ya nemi sauya kungiya watan jiya.

Karin bayani