Manchester United ta ci kazamar riba

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Manchester United na da ratar maki shida tsakaninta da kungiyar da ke ta hudu a teburin premier wato City.

Manchester United ta kama hanyar zama kungiyar kwallon kafa ta farko a Burtaniya da ta samu tara Fam miliyan 500 a cikin shekara guda duk da rashin nasarorin da ta ci karo da su a cikin fili.

Kudaden da kungiyar ta samu a rubu'in na biyu na shekarar bara sun karu da kashi 26.6% idan aka kwatanta da bara; kudin da ya kai Fam miliyan 133 da dubu 800.

A yanzu dai kulob din na United na matsayi na biyar ne a teburin gasar Premier kuma an fitar da shi daga gasar zakarrun Turai.

Haka kuma babu tabbacin kulob din zai cancanci shiga gasar a badi sakamakon matsalolin da ya ci karo da su karkashi jagorancin Louis van Gaal.

Karin bayani