Benteke zai koma Aston Villa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Christian Benteke zai koma Aston Villa, duk da cewa ya dade bai zura kwallo a wasannin shekarar 2016 ba.

Dan wasan gaba Christian Benteke na shirin buga kwallo tsakaninsa da tsohon kulob din sa, Aston Villa a ranar Lahadi, duk da cewa bai zura kwallo ko daya ba cikin wasanni 11 a shekarar 2016.

Dan asalin Belgium din dai yana da goyon bayan kocinsa Liverpool, Jurgen Klopp.

"Ina iya yin abubuwa da dama, ba kuma Christian kadai ba, dole duk wani dan wasa ya taimaki kan sa," in ji Klopp.

Ya kara da cewa, "Na ga alamun nasara sosai lokacin da ya ke West Ham, duk da cewa bai samu da sauki ba, duk da haka akwai yiwuwar za a samu sa'a".