Dimitri ya sa hannu a sabon kwantiragi da West Ham

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sullivan ya ce darajar Dimitri a yanzu ta kai £30 miliyan

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta West Ham, Dimitri Payet mai shekaru 28 ya sanya hannu a kwantiragin shekaru biyar da rabi.

West Ham ta sayi Dimitri daga kungiyar Faransa ta Marseille a kan kudi fam 10 miliyan a lokacin bazara.

Dimitri ya haskaka a kakar wasannin bana, inda ya sanya kwallaye shida a wasanni 22 da ya bugawa Hammers, abin da ya taimaka wa kungiyar zama ta shida a gasar Premier.

Sabon kwantiragin ya maye gurbin tsohon kwantiragin shekaru biyar da dan kwallon ya sanya wa hannu.

A farkon wannan makon ne, West Ham, ta musanta rahotonnin kafafen yada labarai na cewa Dimitri ya matsa lamba yana bukatar sabuwar yarjejeniyar.

Daya daga cikin wadanda suka mallaki kungiyar, David Sullivan ya bayyana Dimitri a matsayin "Kwararren dan wasan da muka dauka a cikin shekaru 25."