Al Nassr ta kori Fabio Cannavaro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fabio Cannavaro ya na cikin tawagar kulob din Italiyar da ta lashe kofin gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2006.

An kori kyeftin din kasar Italiya Fabio Cannavaro a matsayin sa na kocin kulob din Saudiyya Al Nassr, bayan wata hudu kacal yana jagorantarsu.

Cannavaro ya lashe wasanni 14 a matsayin sa na manaja, kuma zai yi sallama da kulob din suna matsayon na shida a gasar kwallon Saudiyya.

Wannan shi ne karo na biyu da yake jagorantar 'yan wasa, bayan watanni bakwai da ya shafe yana manajan kulob din China, Guangzhou Evergrande.

Tsohon mai tsaron baya ya na cikin tawagar Italiya da ta lashe kofin gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2006.

Cannavaro ya yi fice a wasannin da ya buga wa Parma da Juventus da Real Madrid.