PSG ta sabunta kwantiragin Blanc

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blanc ya sanya hannu a kwantiragin da zai bashi damar jagorantar PSG har shekarar 2018.

Kocin Paris St-Germain, ya sanya hannu a sabon kwantiragin da zai bashi damar ci gaba da jagorantar kulob din har zuwa shekarar 2018.

Tsohon mai tsaron baya ya maye gurbin Carlo Ancelloti a watan Yunin shekarar 2013, inda ya jagoranci kulob din a gasar wasanni biyu, ciki har da wasan kakar bara.

A yanzu dai PSG ce kan gaba a gasar Faransa, za kuma su kara da Chelsea a gasar zakarun Turai a wasanni 16 na karshe.

"Ina so in mika godiya ta saboda amanar da aka bani," In ji Blanc.

Ya kara da cewa, "Akwai gasar da har yanzu ta ke mana gizo , watau gasar zakarun Turai, yana kuma da wuyar samun nasara, amma wata rana dai Paris St-Germain za ta lashe gasar."