Sunderland ta kori Adam Johnson

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Johnson da matarsa a hanyarsa zuwa kotu

Sunderland ta sallami Adam Johnson bayan da ya amince da yin lalata da karamar yarinya da kuma tuhumarsa a kan mu'amala da 'yar yarinya.

Dan shekaru 28, kungiyar ta soke kwantaraginsa ne 'yan sa'o'i bayan da aka cire sunansa cikin tawagar Sunderland da za ta fafata da Manchester United.

A ranar Juma'a zai fuskanci kuliya, amma ya musanta zarge-zargen da ake masa.

Kamfanin Adidas mai yin kayan wasa shi me ya soke kwangilarsa da Johnson.

Johnson, wanda aka haifa a Sunderland, ya soma taka leda ne a Middlesbrough kafin ya koma Manchester City daga nan ya koma Sunderland a kan fan miliyan 10 a shekara ta 2012.