Abin da ya sa Leicester ta gagara - Mahrez

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan gefe na Leicester, Riyadh Mahrez

Dan wasan Leicester, Riyadh Mahrez ya ce irin silmiyowar da kungiyar tasa ta yi a kakar wasan gasar Premier da ta gabata ne yasa yanzu take neman gagarar manyan kungiyoyi.

A kakar wasa da ta gabata dai Leicester ta kasance a kasan teburin Premier amma yanzu ita ce ta daya da tazarar maki biyar.

Mahrez ya ce " idan ka sha wahala, to za ka samu ilimin sanin yadda za ka tunkari kalubalen da ke gabanka."

Dan wasan mai shekara 24 ya kara da cewa " a kakar da ta gabata, akwai matsaloli sosai, amma yanzu ba mu da wata matsala."