Sunderland ta wahalar da Man Utd

Image caption kociyan Manchester United, van Gaal

Kungiyar Manchester United wadda take matsayi na 5 a teburin gasar Premier ba ta ji dadin karonta da Sunderland ba mai mataki na 19, a teburin na Premier, ranar Asabar.

An dai tashi daga wasan da ci 2-1, kuma dan wasan Sunderland, Wahbi Khazri ne ya jefa kwallon farko a ragar Manchester United a bugun tazara, minti uku da fara wasa.

Sai dai kuma kafin a tafi hutun rabin lokaci, Anthony Martial ya farke wa Man Utd, kafin Kone ya kara zura kwallo ta biyu a ragar Man Utd din.

Yanzu haka, Manchester United tana da maki 41, a inda ita kuma Sunderland take da 23.