Wellbeck ya fidda Arsenal kunya

Image caption Wellbeck a lokacin da ya jefa kwallo a ragar Leicester

Kwallon da dan wasan Arsenal ya jefa ta biyu a ragar Leicester a mintin karshe na karin lokaci, ita ce ta fitar da Arsenal kunya ta kuma kara sanya kungiyar ta hau saman teburin gasar Premier.

Wellbeck dai ya dawo daga jinya ne sannan kuma wannan ne wasansa na farko tun watan Aprilu na 2015.

Dan wasan Leicester, Jamie Vardy ne dai ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal a bugun fanareti.

Theo Walcott ne kuma ya farkewa Arsenal kafin daga bisani Wellbeck ya kara ta biyu.

Yanzu haka dai tsiran Leicester wanda take saman teburin Premier maki biyu ne kacal tsakaninta da Arsenal.