Rooney da Vardy abin alfahari ne - Hodgson

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roy Hodgson

Kociyan kungiyar wasan kwallon kafa ta Ingila, Roy Hodgson ya ce yana matukar alfahari da irin tashen da 'yan wasan da kungiyar tasa ta rena suke yi a wasannin gasar Premier ta Ingila.

Ya ce irin kwazon da 'yan wasan gaba na Ingila suke yi ya samo asali ne tun lokacin da ya zo kulob din a 2012.

Hodgson ya ce dan wasan Leicester City, Jamie Vardy da Harry Kane na Tottenham sun yi fice wajen cin kwallaye a kakar wasa ta bana.

Har wa yau, ya ce yana kuma samun kwarin gwiwa daga irin kokarin da Wayne Rooney, dan wasan Manchester United yake yi.