Messi: Bugun fanaretin da babu irinsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi da Suarez sun buga fanareti tare

'Yan wasan Bercelona, Lionel Messi da Luis Suarez sun yi wani irin bugun fanareti na musamman domin zura kwallo a ragar Celta Vigo, a wasan da suka tashi 6 da 1 ranar Lahadi.

Shi dai Messi ya yi kamar zai doka kwallon sai ya buga ta gefe, a inda Suarez wanda ke bayansa ya doki kwallon ta kuma fada ragar ta Celta Vigo.

Kuma Messi ya yi hakan ne domin ya ba wa Suarez damar zura cikamakin kwallaye uku, a wasan.

Yanzu haka, Suarez wanda ya zura kwallaye 23 a wasanni 22 na gasar La Liga, shi ne ya fi kowa yawan kwallaye, a gasar a wannan kakar.

Da a ce Messi ya ci kwallon to da za ta kasance kwallonsa ta 300 ke nan ga Bercelona a dukkanin wasannin gasar La Liga.