FIFA za ta saurari koken Platini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Michel Platini

A ranar Litinin ne kwamitin sauraron koke na FIFA zai saurari koken neman sassauci da Michel Platini ya yi dangane da dakatar da shi daga harkokin wasannin har na tsawon shekara takwas.

An dai dakatar da shugaban hukumar kwallon kafa ta turai, Michel Platini, mai shekara 60 daga shugabancin kwamitin da'a na kwallon kafa, a watan Disamba, tare da shugaban hukumar FIFA, Sepp Blatter.

An samu mutanen biyu ne dai da laifin rashawa na $2m da aka ba wa Platini, sai kuma dukka mutanen biyu sun ki amincewa da tuhume-tuhumen.

A ranar Talata ne kuma za a saurari koken Blatter.

Shi dai kwamitin na sauraron koken wanda shugaban kungiyar kwallon kafa ta Bermuda, Larry Mussenden yake jagoranta tana da hurumin rage ko kara ko kuma soke hukuncin dakatarwar da aka yi.