Ba za ta sabu Man City ta hakura da kofi ba - Kompany

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Manchester City ta sha kashi a hannun Leicester da kuma Tottenham

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Vincent Kompany ya ce ba za ta sabu ba, a ce kungiyar ba za ta jajirce ta dauki kofi ba.

Kungiyar Tottenham da ke hamayya da City ce ta zo har gida ta doke City da ci 2-1, abin da yasa Man City ta zama ta hudu kuma tsakaninta da Leicester ya zamanto maki shida ne.

Bugun fanareti da Harry Kane ya ci ne yasa Spurs ta fara samun nasara, kafin daga bisani Kelechi Iheanacho ya farke ta, sai Christian Eriksen ya jefa kwallon da ya bai wa Tottenham nasarar.

Kyaftin din City ya bayyana wa BBC Sport cewa "Babu wani dalilin da zaisa ba zamu jajrice ba domin daukar kofin, akwai bukatar mu kara kaimi."

Sau biyu kenan aka lallasa kungiyar ta Manuel Pellegrini a wasanni uku na gasar Premier, tun bayan da aka sanar da cewa dan kasar Chile zai bar kungiyar, kuma Pep Guardiola zai maye gurbinsa.