Aston Villa: Lescott ya nemi afuwa

Hakkin mallakar hoto rex features
Image caption Dan wasan Aston Villa, Joleon Lescott

Dan wasan baya na Aston Villa, Joleon Lescott ya nemi afuwa dangane da hoton mota mai tsada da ya sanya a shafinsa na twitter bayan da Liverpool ta lallasa kulob din nasa da ci 6 da nema.

Lescott mai shekara 33, ya ce tsautsayi aka samu wajen aike hoton daga wayarsa ta hannu wadda take cikin aljihunsa alhali ya tukun mota.

Sakon da Lescott dai ya jawo ana yi wa kulob din na Aston Villa dariya saboda zazzaga mata kwallaye har shida da Liverpool ta yi, abin da ya sanya kulob din yake tangal-tangal a kasar teburin gasar Premier.

Joleon Lescott ya kara da neman afuwa bisa rashin nasarar da kulob din nasa ya samu.