Doke Leicester tsallake rijiya da baya ne - Wenger

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Arsene Wenger ya yi ta murna, yayin da sauran 'yan wasan Arsenal suka lullube Welbeck

Mai horar da 'yan wasan kungiyar Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana nasarar da kungiyarsa ta samu a kan Leicester a matsayin tsallake rijiya da baya.

Arsenal ta doke Leicester da ci 2-1, a karawar da suka yi a filin wasa na Emirate a ranar Lahadin da ta wuce.

Jamie Vardy dan wasan Leicester ne ya fara zura kwallo a wani bugun fenareti mai takaddama, kafin daga bisani Theo Walcott na Arsenal ya farke ta.

Yayin da Danny Welbeck ne ya zura kwallon da ya bai wa Arsenal nasara, a karin lokacin da aka yi, kuma wasansa ke nan na farko tun bayan wasan da ya buga na karshe a watan Afrilun 2015.

Yanzu dai maki biyu ya rage wa Arsenal ta kamo Leicester, a kan haka Wenger ya ce " Mun sha da kyar daga hannun kungiyar da ta yi fice wajen kare gidanta.