'Yan jarida sun fusata Ronaldo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cristiano Ronaldo ya ce babu dan wasan da ya fi shi zura kwallaye a Madrid.

Dan wasan gaba na Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya fice daga wajen wani taron manema labarai bayan an tambaye shi me ya sa ba ya zura kwallo idan suka buga wasa a gidan wata kungiyar.

Ronaldo, mai shekara 31, ya ci kwallo 32 a kakar wasa ta bana amma bai zura kwallo ko da guda daya ba a wasannin da suka buga a gidan wata kungiyar ba tun daga ranar 29 ga watan Nuwamba.

Gabanin ya fice daga wajen taron, Ronaldo ya ce, "Wa nene ya zura kwallaye fiye da ni a gidan wata kungiya tun da na zo Spain? Ku gaya min dan wasa daya da ya fi ni zura kwallo. Baku da amsa? To, na gode".

Ronaldo ya yi taron maneman labaran ne ranar Talata gabanin wasan da za su yi da Roma na Gasar cin Kofin Zakarun Turai a ranar Laraba.